{"id":2739,"date":"2024-08-25T12:08:14","date_gmt":"2024-08-25T12:08:14","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2739"},"modified":"2024-08-25T12:08:15","modified_gmt":"2024-08-25T12:08:15","slug":"da-alama-za-a-kwashe-shekaru-masu-yawa-ana-yaki-a-sudanya%c6%99in-sudan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2739","title":{"rendered":"Da Alama Za a Kwashe Shekaru Masu Yawa Ana Yaki a SudanYa\u0199in Sudan."},"content":{"rendered":"\n<p> ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda dubbai suka yi gudun hijira zuwa \u0199asashen ma\u0199ota, yayin da aka kashe dubbai.Dakarun sojin Sudan \u0199ar\u0199ashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan sun kwashe watanni 16 suna fafatawa da maya\u0199an rundunar kai \u0257aukin gaggawa ta Rapid Support Forces.<\/p>\n\n\n\n<p>Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Switzerland ba da rundunar kai \u0257aukin gaggawa ta \u0199asar, yana mai cewa maimakon haka za su kwashe &#8220;shekara 100 suna ya\u0199i.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ba za mu je Geneva ba&#8230; za mu kwashe shekara 100 muna ya\u0199i,&#8221; in ji Burhan, wanda dakarunsa suka kwashe watanni 16 suna fafatawa da maya\u0199an rundunar kai \u0257aukin gaggawa ta Rapid Support Forces. <\/p>\n\n\n\n<p>Ya bayyana haka ne ga manema labarai ranar Asabar a Port Sudan.Amurka ta bu\u0257e wani shirin tattaunawa a Switzerland ranar 14 ga watan Agusta da zummar kawo \u0199arshen bala&#8217;in da ya\u0199i ya jefa \u0199asar ta Sudan.<\/p>\n\n\n\n<p>Wakilan RSF sun halarci wurin tattaunawar, sai dai gwamnatin Sudan ba ta amince da tsarinsa ba, kuma ba ta je wurin taron ba, ko da yake ta yi magana ta wayar tarho da masu shiga tsakani.Saudiyya da Switzerland, da Tarayyar Afirka da Masar da Ha\u0257a\u0257\u0257iyar Daular Larabawa da Majalisar \u018ainkin Duniya na cikin mahalarta taron wanda ke neman samar da dawwamammen zaman lafiya a Sudan.<\/p>\n\n\n\n<p>Sun kammala taron ranar Juma&#8217;a ba tare da cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ba ko da yake an samu ci gaba game da shigar da kayan agaji \u0199asar ta wasu muhimman hanyoyi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya\u0199in Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda kimamin mutum miliyan 25 a fa\u0257in \u0199asar suke fama da bala&#8217;in yunwa.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda dubbai suka yi gudun hijira zuwa \u0199asashen ma\u0199ota, yayin da aka kashe dubbai.Dakarun sojin Sudan \u0199ar\u0199ashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan sun kwashe watanni 16 suna fafatawa da maya\u0199an rundunar kai \u0257aukin gaggawa ta Rapid Support Forces. Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2740,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2739","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2739","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2739"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2739\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2741,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2739\/revisions\/2741"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2740"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2739"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2739"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2739"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}