{"id":2718,"date":"2024-08-24T09:39:23","date_gmt":"2024-08-24T09:39:23","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2718"},"modified":"2024-08-24T09:39:23","modified_gmt":"2024-08-24T09:39:23","slug":"an-sami-ambaliyar-a-nigar-da-rayi-tafiyar-ruwa-da-wasu-manyan-tituna-a-birnin-yamai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2718","title":{"rendered":"An Sami Ambaliyar a Nigar Da Rayi Tafiyar Ruwa Da Wasu Manyan Tituna a Birnin Yamai."},"content":{"rendered":"\n<p>Manyan hanyoyin shiga da fita daga Yamai babbar birnin Jamhuriyar Nijar sun kusan katsewa baki \u0257aya daga sauran sassan \u0199asar sakamakon iftila&#8217;in ambaliyar ruwa da ya mamaye yankin Sahel tun daga watan Yuni.<\/p>\n\n\n\n<p>Kwalekwale sun maye gurbin motocin da babura a kan hanyoyin sakamakon ambaliyar ruwa da tamamaye\u00a0 Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.<\/p>\n\n\n\n<p>Manyan hanyoyin fita da shiga birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar mai kimanin mutum miliyan 1.5 sun kusan katsewa ba\u0199i \u0257aya, kana sama da mazauna birnin mutum 11,500 ne iftila&#8217;in ambaliyar ruwan sama ya shafa.A watanni uku da suka wuce, ambaliyar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 217 a fa\u0257in \u0199asar kana ta shafi sama da mutane 350,000, a cewar gwamnatin mulkin soji ta Nijar.<\/p>\n\n\n\n<p>Da farko dai birnin Yamai ya tsira daga sauran yankunan kudu maso yammacin Nijar, amma a yanzu, kwale-kwale ne suka maye gurbin \u0199anana da manyan motoci da babura wajen jigilar mutane da kayayyaki a kan hanyoyi.<\/p>\n\n\n\n<p>Don samun damar isa zuwa ga sauran sassan \u0199asar, &#8221;dole sai mutum ya yi amfani da kwale-kwale tare da fatan samun abin hawa idan ya isa \u0257aya bangaren,&#8221; in ji Habibulaye Abdoulaye, wani mazaunin wata unguwa da ke kewaye da ruwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Yawancin kamfanonin sufuri a Yamai sun dakatar da zirga-zirga zuwa sauran sassan Nijar.Yayin da yake kallon yadda ambaliyar ruwan ke gudu ta gefen birnin, wani direban mota Ali Adamou ya shaida wa kamfanin dillacin labarai Faransa AFP cewa ruwan ya tafi da motarsa tare da wasu guda hudu.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Na kusan mutuwa a lokacin da wata \u0199aramar motar bas ta nutse,&#8221; in ji A damou Gyara hanyoyi Masu tu\u0199a \u0199ananan jiragen ruwa suna kar\u0253ar CFA 500 kan duk jigilar da suka yi sai kuma &#8216;yan sanda da kwale-kwalen sojoji wa\u0257anda suke taimakawa wajen jigilar mazauna da suka ma\u0199ale.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga gabashin babban birnin \u0199asar, kamfanin gine-gine na \u0199asar Faransa Sogea-Satom na \u0199o\u0199arin sake bu\u0257e hanyar \u0199asa ta \u0257aya, babbar hanyar da ta kai tsawon kilomita 1,500.<\/p>\n\n\n\n<p>A ga\u0253ar kogin Neja da ke birnin Yamai, masu aikin tono suna can suna aikin samar da hanyoyin wucewar ruwan, yayin da masu aikin sa kai da sojoji suke zagayawa don toshe wurare da ruwan ya yi wa illa da yashi.<\/p>\n\n\n\n<p>A kwanakin baya ne aka sake bu\u0257e hanya \u0257aya tilo ta Tera da manyan motoci suke wucewa daga Yamai zuwa arewacin Burkina Faso.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Hukumomin jihar suna yin dukkan mai yiwuwa don maido da zirga-zirgar ababen hawa,&#8221; in ji Ministan Sufuri, Kanar Salissou Mahaman Salissou.<\/p>\n\n\n\n<p>Hukumomin Nijar dai na fargabar tsawaita zirga-zirgar na iya haifar da \u0199aranci man fetur.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Manyan hanyoyin shiga da fita daga Yamai babbar birnin Jamhuriyar Nijar sun kusan katsewa baki \u0257aya daga sauran sassan \u0199asar sakamakon iftila&#8217;in ambaliyar ruwa da ya mamaye yankin Sahel tun daga watan Yuni. Kwalekwale sun maye gurbin motocin da babura a kan hanyoyin sakamakon ambaliyar ruwa da tamamaye\u00a0 Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar. Manyan hanyoyin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2719,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2718","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2718","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2718"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2718\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2720,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2718\/revisions\/2720"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2719"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2718"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2718"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2718"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}