{"id":2637,"date":"2024-08-20T17:41:18","date_gmt":"2024-08-20T17:41:18","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2637"},"modified":"2024-08-20T17:41:19","modified_gmt":"2024-08-20T17:41:19","slug":"ambaliyar-ruwa-mutum-129-sun-mutu-yayin-da-sama-da-120-suka-jikkata-a-nijar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2637","title":{"rendered":"{AMBALIYAR RUWA} MUTUM 129 SUN MUTU YAYIN DA SAMA DA 120 SUKA JIKKATA A NIJAR."},"content":{"rendered":"\n<p> Iftila&#8217;in ambaliyar ruwan sama a Nijar ya yi sanadin mutuwar mutum 129, yayin da wasu mutum 126 kuma suka jikkata, a cewar Hukumar shirye-shirye da gargadi da kuma ta\u0199aita aukuwar bala&#8217;o&#8217;i tare da kare al&#8217;umma (DPA\/GC) a \u0199asar.\u00a0<\/p>\n\n\n\n<p>Mutane da dama sun mutu a ambaliyar ruwa a Nijar, yayin da wasu kuma suka jikkata \/ Hoto: AFPMummunan iftila&#8217;in ambaliyar ruwa a Nijar ya yi sanadin mutuwar mutane da dama yayin da wasu kuma suka jikkata tun da aka shiga lokacin daminar bana a \u0199asar.<\/p>\n\n\n\n<p>Hukumar shirye-shirye da gargadi da kuma takaita aukuwar bala&#8217;o&#8217;i tare da kare al&#8217;umma (DPA\/GC) a Nijar, ta ce ya zuwa 12 ga watan Augusta, 2024 iftila&#8217;in ya yi sanadin mutuwar mutum 129, yayin da wasu mutum 126 kuma suka jikkata.Rahotanni sun yi nuni da cewa, al&#8217;ummomi 28,000 ne iftila&#8217;in ya shafa, yayin da gidaje 23,619 suka rushe sannan an yi asarar dabbobi 16,000, kamar yadda kafar yada labarai ta Actuniger ta rawaito.<\/p>\n\n\n\n<p>Yawan adadin da \u0253arnar ta haifar ya \u0199aru sosai idan aka kwatanta da adadin da ministar ayyukan jin\u0199ai da takaita aukuwar bala&#8217;o&#8217;i a Nijar, Madam Aissa Laouan Wandarama ta bayyana ya zuwa ranar 7 ga watan Agusta.<\/p>\n\n\n\n<p>Rahoton bayanan da aka tattaro a lokacin ya yi nuni da cewa, mutum 94 ne suka mutu, daga ciki an rasa 44 daga kai-tsaye sakamakon ambaliyar ruwan, yayin da 50 kuma suka mutu a ruftawar gidaje.<\/p>\n\n\n\n<p>Kazalika adadin mutanen da lamarin ya shafa a lokacin ya kai 137,156, inda gidaje 14,045 suka rushe sai kuma \u0253ukkoki 502 sun lalace.<\/p>\n\n\n\n<p>An kuma yi asasar dabbobi 15,470, daga ciki akwai \u0199ananan dabbobin gida 13,981 da kuma manya 297.Sannan ambaliyar ta shafe kadada 2,763 na gonakin noma a Nijar, inda aka yi asarar ton 17,495 na kayan amfanin gona tare da jikkata mutane 93.<\/p>\n\n\n\n<p>Rahotannin baya-bayan nan dai sun nuna yadda iftila&#8217;in ya haifar da mummunar barna a kusan dukka fa\u0257in yankunan Nijar, inda ta shafi ababen more rayuwa tare da katse hanyoyin tafiye-tafiye a \u0199asar.\u0198ididdigar hasashen yanayi ta yi nuni da cewa akwai yiwuwar iftila&#8217;in ambaliyar ruwa a shekarar 2024 a yankunan Yammaci da tsakiyar Afirka ya zarce na shekarun baya.Ta kuma ce hakan zai ta&#8217;azzara yanayin da al&#8217;ummomi ke ciki matukar ba a \u0257auki matakan da suka kamata ba bisa ga tsarin kariya da muhimman matakan takaita tasirin sauyin yanayi da hukumomi suka bayar.<\/p>\n\n\n\n<p>TRT Afrika<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Iftila&#8217;in ambaliyar ruwan sama a Nijar ya yi sanadin mutuwar mutum 129, yayin da wasu mutum 126 kuma suka jikkata, a cewar Hukumar shirye-shirye da gargadi da kuma ta\u0199aita aukuwar bala&#8217;o&#8217;i tare da kare al&#8217;umma (DPA\/GC) a \u0199asar.\u00a0 Mutane da dama sun mutu a ambaliyar ruwa a Nijar, yayin da wasu kuma suka jikkata \/ [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2638,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2637","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2637","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2637"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2637\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2639,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2637\/revisions\/2639"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2638"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2637"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2637"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2637"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}