{"id":2572,"date":"2024-08-16T14:02:03","date_gmt":"2024-08-16T14:02:03","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2572"},"modified":"2024-08-16T14:02:03","modified_gmt":"2024-08-16T14:02:03","slug":"nijeriya-ta-zargi-wani-kamfanin-kasar-china-da-kokarin-kwace-kadarorin-gwamnati","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2572","title":{"rendered":"NIJERIYA TA ZARGI WANI KAMFANIN KASAR CHINA DA KOKARIN KWACE KADARORIN GWAMNATI."},"content":{"rendered":"\n<p>Nijeriya ta zargi wani kamfani na kasar China da \u0199o\u0199arin \u0199wace kadarorin gwamnatin tarayya ba bisa \u0199a&#8217;ida ba bayan wata ta\u0199addama da jihar Ogun.Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce a ranar 15 ga watan Agusta, 2024, tana aiki tare da jihar Ogun domin warware rikicin da kuma kare kadarorin kasar daga \u0199wacewa. <\/p>\n\n\n\n<p>Fadar Shugaban Nijeriya da Gwamnatin Nijeriya ta zargi wani kamfanin \u0199asar China da yun\u0199urin \u0199wace kadarorinta a \u0199asashen \u0199etare ciki har da jiragen Shugaban \u0198asa, kamar yadda kakakin shugaban \u0199asar ya bayyana a ranar Alhamis.Mai magana da yawun Shugaban \u0198asar, Bayo Onanuga, ya ce Kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Ltd yana amfani da \u201chanyar da ba ta dace ba\u201d wajen \u0199o\u0199arin \u0199wace kadarorin gwamnatin Nijeriya, duk da cewa ba shi da wata ala\u0199a ta kwangila da gwamnatin tarayyar.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamfanin Zhongshan bai mayar da martani ba nan-take.Ta\u0199addamar dai ta samo asali ne daga wata kwangilar da Zhongshan ya \u0199ulla da jihar Ogun ta kudu maso yammacin Nijeriya a shekarar 2007, ta samar da yankin kasuwanci marar shinge, wanda aka soke a shekarar 2015.&#8217;Babu \u0199a\u0199\u0199arfar hujja&#8217; Onanuga ya ce lokacin da aka soke kwantiragin jihar Ogun a shekarar 2015, abin da Zhongshan ya yi na aikin bai wuce gina katanga ba a filin da aka ke\u0253e domin gina yankin kasuwanci marar shingen. \u201cZhongshan ba shi da \u0199wa\u0199\u0199warar hujjar da zai bu\u0199aci gwamnatin jihar Ogun ta biya shi bisa hujjar kwangilar da aka \u0199ulla tsakanin kamfanin da gwamnatin jihar a shekarar 2007 don gina yankin kasuwanci marar shinge,\u201d in ji Onanuga.<\/p>\n\n\n\n<p>Gwamnatin Nijeriyar dai ta ce ba ta cikin wannan kwangilar, kuma Zhongshan ya gabatar da wasu hujjoji da ba daidai ba a gaban kotuna a Birtaniya, da Amurka, da kuma Faransa, inda kotu ta ce a biya shi dala miliyan 60 a matsayin diyya.Nijeriya ta \u0199i biyan wa\u0257annan ku\u0257a\u0257e, in ji Onanuga.<\/p>\n\n\n\n<p>Kadarorin da ba su da kariyaOnanuga ya ce, Zhongshan ya samu umarni biyu daga wata kotun Faransa a watan Maris da Agusta na \u0199wace kadarorin Nijeriya, ciki har da jiragen Shugaban \u0198asa da ake kula da su a Faransa. Ya ce wa\u0257annan kadarorin ba su da kariya daga ayyukan shari&#8217;a na \u0199asashen waje.<\/p>\n\n\n\n<p>Gwamnatin Nijeriya na aiki tare da jihar Ogun domin shawo kan rikicin da kuma kare kadarorin \u0199asar da aka \u0199wace, <\/p>\n\n\n\n<p>TRT AFRIKA, in ji Onanuga.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Nijeriya ta zargi wani kamfani na kasar China da \u0199o\u0199arin \u0199wace kadarorin gwamnatin tarayya ba bisa \u0199a&#8217;ida ba bayan wata ta\u0199addama da jihar Ogun.Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce a ranar 15 ga watan Agusta, 2024, tana aiki tare da jihar Ogun domin warware rikicin da kuma kare kadarorin kasar daga \u0199wacewa. Fadar Shugaban Nijeriya da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2573,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2572","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2572","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2572"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2572\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2574,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2572\/revisions\/2574"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2573"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2572"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2572"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2572"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}