{"id":2437,"date":"2024-08-04T08:53:34","date_gmt":"2024-08-04T08:53:34","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2437"},"modified":"2024-08-04T08:57:25","modified_gmt":"2024-08-04T08:57:25","slug":"muhimman-abubuwan-da-shugaba-tinubu-ya-bayyana-yan-nigeria-akn-zanga-zangar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2437","title":{"rendered":"MUHIMMAN ABUBUWAN DA SHUGABA TINUBU YA BAYYANAWA &#8216;YAN NIGERIA AKN ZANGA-ZANGAR"},"content":{"rendered":"\n<p><\/p>\n\n\n\n<p>Shugaba Tinubu ya ce yana sane cewa janye tallafin fetur zai sa ya fuskanci \u0199alubale, &#8220;amma ina tabbatar muku cewa na shirya fuskantar kowane irin \u0199alubale muddin zai samar da kyakkyawan shugabanci ga al\u2019ummar Nijeriya.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa tana bayar da tallafi ga manoma domin samar da \u0199arin abinci.<\/p>\n\n\n\n<p>Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa ta janye tallafin man fetur ne a yun\u0199urinta na bun\u0199asa tattalin arzikin \u0199asar da kawar da masu yi mata &#8220;zagon-\u0199asa&#8221; duk kuwa da ra\u0257a\u0257in da hakan ke haifarwa ga &#8216;yan \u0199asar.<\/p>\n\n\n\n<p>Shugaban ya bayyana haka ne ranar Lahadi 4 a jawabin da ya yi wa &#8216;yan Nijeriya ta gidan talbiji<\/p>\n\n\n\n<p>Na ji ciwon irin asarar rayuka da aka yi a wasu jihohi, irin su Borno, Jigawa, Kano, Kaduna da dai sauransu, da \u0253arnata dukiyoyin jama&#8217;a a wasu jihohin, kai har ma da yadda aka ri\u0199a wawushe manyan kantuna da shaguna, sa\u0253anin al\u0199awarin da masu shirya zanga-zangar suka yi cewa, zanga-zangar za ta kasance cikin lumana a fa\u0257in \u0199asarmu.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-gallery has-nested-images columns-default is-cropped wp-block-gallery-1 is-layout-flex wp-block-gallery-is-layout-flex\">\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"575\" data-id=\"2438\" src=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/08\/IMG-20240804-WA0002-1024x575.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2438\" srcset=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/08\/IMG-20240804-WA0002-1024x575.jpg 1024w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/08\/IMG-20240804-WA0002-300x169.jpg 300w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/08\/IMG-20240804-WA0002-768x431.jpg 768w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/08\/IMG-20240804-WA0002-860x483.jpg 860w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/08\/IMG-20240804-WA0002.jpg 1280w\" sizes=\"auto, (max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><\/figure>\n<\/figure>\n\n\n\n<p>A matsayina na shugaban wannan \u0199asa, wajibi ne na tabbatar da doka da zaman lafiya. Kamar yadda kundin tsarin mulkin \u0199asar nan ya \u0257ora min alhakin hakan kuma na amince, da cewa zan kare rayuka da dukiyoyin kowane \u0257an \u0199asa, don haka gwamnatinmu ba za ta saka ido ta bar wasu tsiraru masu \u0253oyayyiyar manufa ta siyasa su wargaza wannan \u0199asa mai albarka ba.<\/p>\n\n\n\n<p>A wannan yanayi da ake ciki, ina ba masu shirya wannan zanga-zangar da ma masu yinta umarni, da su dakatar da duk wata zanga-zanga, su maye gurbinta da bu\u0257e \u0199ofar tattaunawa da sulhu, wanda a ko da yaushe \u0199ofata a bu\u0257e take ga hakan.<\/p>\n\n\n\n<p>Na tsinci kaina a yanayin da ba ni da za\u0253in da ya wuce na ya \u0257auki matakin da ya dace duk da ra\u0257a\u0257insa, don haka na cire tallafin man fetur da kuma kawar da tsarin musayar ku\u0257a\u0257en waje da yawa wa\u0257anda suka haifar da tsaiko da cikas ga tsarin tattalin arzikin \u0199asarmu da ci gabanta da namu.<\/p>\n\n\n\n<p>Wa\u0257annan matakai da na \u0257auka sun toshe duk wata ribar da \u2019yan fasa-\u0199wauri da masu yi wa \u0199asarmu zagon-\u0199asa suke samu. Haka kuma sun toshe tallafin da muka bai wa \u0199asashen da ke ma\u0199wabtaka da mu na a-sai-da-rai-a-nemo-suna, da tuni kafin mu farga sun mayar da tattalin arzikinmu kashin-baya. E! Na yarda, hakan zai haifar min da \u0199alubale. Amma ina tabbatar muku cewa na shirya fuskantar kowane irin \u0199alubale muddin zai samar da kyakkyawan shugabanci ga al\u2019ummar Nijeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Mun fitar da sama da Naira biliyan 570 ga jihohi 36 domin fa\u0257a\u0257a shirye-shiryensu na tallafawa rayuwar al&#8217;ummomin jihohinsu, yayin da \u0199ananan \u2018yan kasuwa 600,000 suka ci gajiyar tallafinmu, ana sa ran \u0199arin \u0199ananan &#8216;yan kasuwa 400,000 su ma za su amfana.<\/p>\n\n\n\n<p>Gwamnatinmu ta bai wa matasa kulawa ta hanyar kafa tsarin rance ga \u0257alibai mai suna NELFUND. Yanzu haka an fitar da ku\u0257i da ya kai Naira biliyan 45.6 ga \u0257alibai da cibiyoyinsu daban-daban, kuma ina kira tare da \u0199arfafa gwiwa ga \u0199wararrun matasanmu da su yi amfani da damarsu wajen cin gajiyar shirin.<\/p>\n\n\n\n<p>Mai rahoto;<br>Musa Badamasi Gama.<br>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Tinubu ya ce yana sane cewa janye tallafin fetur zai sa ya fuskanci \u0199alubale, &#8220;amma ina tabbatar muku cewa na shirya fuskantar kowane irin \u0199alubale muddin zai samar da kyakkyawan shugabanci ga al\u2019ummar Nijeriya.&#8221; Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa tana bayar da tallafi ga manoma domin samar da \u0199arin abinci. Shugaban Nijeriya Bola [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2439,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2437","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2437","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2437"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2437\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2443,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2437\/revisions\/2443"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2439"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2437"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2437"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2437"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}