{"id":2377,"date":"2024-07-30T16:34:55","date_gmt":"2024-07-30T16:34:55","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2377"},"modified":"2024-07-30T16:34:58","modified_gmt":"2024-07-30T16:34:58","slug":"inuwar-jamaar-arewa-saqo-na-musamman-game-da-zanga-zangar-tsadar-rayuwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2377","title":{"rendered":"INUWAR JAMA’AR AREWA. Saqo na Musamman game da Zanga Zangar Tsadar Rayuwa"},"content":{"rendered":"\n
ZANGA- ZANGAR TSADAR RAYUWA
Zanga-zanga yancin yan kasa wanda tsarin mulki ya basu domin baiyana damuwar su ga gwamnati cikin abin da basu da wata hanyar baiyana kokensu ko kuma saboda kin karban kukansu tahanyar wakilan su.
Zanga zanga nau\u2019i biyu ce zanga-zangar lumana da zanga-zanga tarzoma, kundin tsarin mulki ya amince yan kasa suyi zanga zanga lumana domim baiyana bukatunsu da damuwarsu ga gawmnatocinsu wanda zaayi ta lafiya kuma a gama lafiya ba tare da an taba kayan kowa, ko kuma an cutar da wani ba. duk wata zanga zanga da za a gabatar ta zama sanadin asarar dukiya da salwantar rayuwa da raunata jama\u2019a ba ta dace masu hankali su amince da ita ba, kuma babu wata gwamnati da zata yarda ta kuma amince da ita
Jama\u2019ar taraiyar Najeriya akarkashin kundin tsarin mulki sun fito sun zabi shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu da mataimakin sa kashim shattima a karkashin tsarin damokradiyya.
A jawabin shugaban kasa na farko bayan rantsar dashi ya sanar da cire tallafin man fetir wanda hakan yazama sanadiyar tashin farashin kayan abinci da sauran abubuwan rayuwar yau da kullum, wanda kuma yayi sanadin shiga halin kunci da kakanikayi musamman ga talakawa.
Talakawa a Najeriya sun shiga halin matsanancin kuncin rayuwa da karyewar tattalin arziki da tabarbarewar al\u2019amuran rayuwa, wanda abin da zasu ci yake nema ya gagaresu dasu da iyalin su, Talakawa yan kasuwa da kananan ma\u2019aikata da masu sana\u2019ar hannu abin da suke samu a wata baya isar su su ci abinci sau biyu dasu da iyalinsu na tsawon sati biyu , wanda hakan kuma ya jefa rayuwar mata da tsofaffi da kananan yara da basu da sana\u2019a ko aikin yi cikin mayuwacin hali da bashi da misali.
A wanan hali da talakawa suke ciki babu wanda yake da nutsuwa da sauran walwala, kowa ka gani kuka yake, kuma duk wani mai wata sana\u2019a ko kayan sayarwa ya tsuga kudi akan kayansa domin ya samu abin da zai rayu dashi da iyalansa, wanda hakan ya kara jefa rayuwar talakawa cikin garari da takaici
Gwamnati ana ta bangaren ta baiyana wa yan kasa cewa ta cire tallafin man fetur ne domin habaka tattalin arziki wanda yake neman durkushewa, kuma tayi hakan ne domin amfanin jama\u2019ar kasa baki daya. Amaimakon tallafin da take bayarwa a baya wanda wasu tsirarune sue amfana dashi.
Su kuma talakawa ana su bangaren suna ganin cire tallafin man shine ummul aba\u2019isin jefa su wannan mawuyacin hali da suke ciki, akan haka suke kira ga gwamnati data dawo da tallafin da ta cire domin kowa ya samu saukin rayuwa da kuma walwala.
Wannan jayaiyar tsakanin gwannati da talakawa ta fara tun satin farko da gwamnati ta cire tallafin wanda ita kuma gwamnati tace \u201cMaganar cire tallafi babu gudu babu ja da baya\u201d sai dai yau kimanin shekara guda da wani abu kullum matsololin rayuwa karuwa suke talakawa suna kara shiga wahalhalu da basu san ranar fita ba. ita kuma gwamnati a nata bangaren tana kara bawa talakawa hakuri tare da albishir na samun saukin rayuwa anan gaba da kuma sanar da bude bodogi da kuma cire haraji ga masu shigo da kayan abinci da alkawarin tallafawa manoma da taki da kayan aiki da kuma samarwa da matasa hanyoyin dogaro da kai damin samarwa da yan kasa saukin rayuwa.
Ana cikin wannan hali sai ga wasu kiraye-kiraye ta kafofin sadarwa na zamani da ke baiwa gwamnati wa\u2019adin wata guda akan ta dawo da tallafin mai ko kuma a shiga zanga-zangar sai \u201cbaba ta gani\u201d.
sakamakon halin kunci da talakawa suka samu kansu na rashin abinci da magani da rashin samun halin zirga-zirga da sauran mu\u2019amalolin rayuwa sai suke fara gowon bayan wadannan kiraye-kiraye ba tare da sanin daga ina suka fito ba, su wane ne jagororin da zasu jagoranci zanga-zangar, menene manufarsu, menene sakamakon da zai biyo bayan zanga-zangar.
Ganin yadda matasa suka karbi kiraye-kirayen fitowa zanga sai malamai da shugabannin alumma suka fara yin bayanin matsayin zanga-zangar da kuma illarta tare da bayar da misalai na munanan abubuwa da suka biyo bayan zanga-zangar da aka yi a wasu kasashen na kusa da kuma na nesa.
Maganganun da iyayen mu, malamai da shugabanni suka farayi na hadarin da yake ckin yin zanga-zangar da rahin dacewar ta da koyarwar addinin mu, sai wasu fusatattun matasa suka fara mai da masu da martini na batanci kamar ka ce da yardarsu koda amincewarsu da goyon bayansu ne talakawa suka shiga halin da suke ciki, wanda hakan shine zai kasance mafi girman kuskuren da matasan arewa zasu yi wato bijirewa shugabaninsu da malaman su saboda kiraye-kirayen mutanen da basu sani ba basu san manufarsu ba kuma basu taba amfanar da rayuwarsu da komai ba.
Yin zanga zangar lumana Kamar yadda dokar kasa ta amince da ita ba laifi bane, Kuma ta sharia baza ta haramta ba ko da kuwa bata rike ta a matsayin hanyar samun bukata Ko fita daga wani tsanani ba.
Domin a tsarin addinin musulunci shugabanci amana ce kuma yin adalci wajibine kawar da duk wani abu da Zai cutar da talakawa ya kuntata rayuwarsu nauyi ne akan kowanne shugaba a kowanne hali domin ita Sharia da gwamnati an samar da sune domin su karewa dukkanin almunma manyan abubuwa guda biyar:-
RAYUKANSU
DUKIYOYINSU
HANKULANSU
NASABARSU
MUTUNCINSU .
Tabbatar da kariya ga wadannan abubuwa guda biyar shine mafi girman wajibin dake kan ko wanne shugaba da dukkanin damar da yake da ita da gwargwadon halin da yasamu kansa. Wannan ita ce siyasa a musulunci Kuma shine aikin gwamnati kuma domin tabbatar da kare wadannan hakkoki guda biyar ne aka samar da dokoki na kisar kai da sata da zina da shan giya ko kwayoyi da kuma cin zarafin mutane .
Shima Kuma biyaiya ga shuwagabanni da kaucewa tarzoma da tashin hankali amanace akan talakawa domin gudun fadawa cikin yake-yake wanda zaiyi sanadiyar zubar da jinane da asarar dukiyoyi da baa san adadin su ba.
A tsarin addinin Musulunci zaluncin shugabanni ga talakawa haramun ne haka shima tawaye ga shugabanni haramun ne, Kuma Ko da talakawa sun gamu da azzaluman shuwagabanni baya halatta suyi musu tawaye da fito na fito domin gudun abin da zai biyo baya na assarar rayuka da rikicewar rayuwa wanda shine yafi zaluncin girma da kuma muni.
Wannan kuma shine ma\u2019auni da iyayen mu, malamai da sarakuna da sauran jagororin suka gina maganganunsu da shawarworinsu ga alummar kasa. A cikinsu babu wanda yake goyon bayan halin matsatsi da ake ciki babu wanda aka yi shawara dashi yayin cire tattalin man fetur babu Kuma wanda wannan yanayin bai shafe Shi ba, Amma a matsayin su na jagorori babu yadda zasu goyi bayan wasu mutane da ba a san Ko su wanene ba ? ba\u2019san daga Ina suke ba? Kuma ba\u2019a san menene munufarsu ba? kuma baa san Su wanene suka daukan nauyinsu ba? Su jafe alummar su cikin musiba, al hali muna da wasu hanyoyin masu yawa wadanda kuma suka fi zanga\u2013zangar sauki da amfani wadanda kuma basu da hadarin da zanga-zangar take da shi kuma suka fita tabbas.
Shin wadanda suke shirin fita wannan zanga-zangar sun tambayi kan su wadan tabayoyin.
Shin mu da zamu fito zanga-zangar lumana. domin gwamnati ta dawo mana da tallafin mai, domin samun saukin rayuwa Babu wata hanyar da tafi dacewa mu nemi wannan bukatan namu a wajen Gwamnati sai ta hanyar Zanga-zanga muna da tabbacin zanga-zangar da zamu gabatar zata sanya gwamnati ta dawo da tallafin data cire?,
Idan gwamnati bata dawo da tallafin ba har tsawon kwana nawa zamuyi mu hakura mu ma Koma gida.
Shin muna da cikakken iko akan dukkanin wadanda zasu fito zanga-zangar
Idan kuma aka fara zanga-zangar lumana wasu suka fara afka wa dukiyoyin jama\u2019a dafasa kayan gwamnati shin muna dawani shiri akan dakatar dasu.
Idan kuma muka kasa dakatar dasu muna zaton jami\u2019an tsaro zasu zuba idansu suna kallo.
idan kuma wasu suka fara tayar da tarzoma sai jamian tsaro suka dauki mataki akan su menene zai biyo baya daga masu zanga-zangar.
Idan Kuma masu zanga-zangar suka fara Mai da martani ga jami\u2019an tsaro wanne mataki muke zato gwamnati zata dauka?
Kuma menene ribar yan kasa da gwamnati idan al\u2019amrin ya tafi a haka?.
Kuma wanene alhakin rayukan jama\u2019a da dukiyoyin su yake kansu?
Kuma zuwa yaushe ne muke da tabbacin komai zai kare kowa ya koma ya cigaba da harkokinsa.
A tsohon zamanin da za\u2019a dauka ana zanga-zangar menene ma komar talakawa da sai sun fita zasu samu abincin da zasu ci?
Wanene zai dauki nauyin basu abinci da saura bukatun rayuwarsu?
Idan kuma tarzoma ta faru a kasar sakamakon zanga-zangar ina masu zanga-zangar suka tanadar wa yan kasar domin gudun Hijira?
Ta wacce hanyar zasu fitar dasu kuma da wanne tanadi sukayi musu na abubuwan hawa da zasu kwashe su?
Idan kuma gwamnati ta fadi wanene suka shirya zai zama shugaban kasa, Shin jama\u2019ar kasa zasu karbe shi?
Idan kuma wasu daga alummar kasa basu karbe shi ba, Ya za\u2019ayi da su, Idan suma suka fito suna zanga- zanga da kone kone da kashe kashe zaa tura musu jami\u2019an tsaro su tarwatsa su
Idan kuma suma suka kifar da gwamnatin wanene zai zama shugaban kasa na gaba kuma menene tabbacin dorewar hadin kan kasar kamar yadda take?
Kuma wanne shiri muke dashi na hana yan ta\u2019adda shigowa cikin zanga-zangar domin cigaba da taadancin su?
Idan kuma wasu daga kasashen waje suka yi amfani da sojojin haya domin rusa kasar ya zaku kare kasar da jamaar kasar daga taaddacin su?
Matukar zaku amsa mana wadannan tambayoyi da gamsasun hujjoji da tabbacin samun nasarar zanga-ziangar ba tare da wata tarzoma ba, da daukar matakin hana faruwar duk wani mummunan abu akasar mu muma muna goyon bayan zanga-zangar ko bamu shiga ciki ba zamu rika fitowa muna daga muku hannu muna baku ruwan sanyi da Dabino amma duk wanda ya tabbatar bashi da amsar wadannan tambayoyi ya kiyayi kansa da shiga wannan zanga-zanga da bata da kai Kuma bata da alkibla.
A matsayin mu na alumma ya zama wajibi mu hada kanmu mu nemi mafita da tadace ta hanyar anfani da ilimi, hikima da jagoranci batare da cutar da wani ko jefe kai cikin hadari ba.
A dangane da ita gwamnati ya zama wajibi ta sauke nauyin da Allah ya dora mata ta kiyaye aikata duk wani abu da zai jefa rayuwar yan kasa cikin garari da damuwa domin biyan bukatar wasu makiya daga kasashen waje ko wasu masu son zuciya daga tsirarun yan kasa, domin shugabanci anayinsa ne domin samar da maslaha ga al\u2019umma baki daya ba wasu tsirarun mutane ba.
Nijeria kasarmu ce baki daya mazan mu da mata talakawa da mawadata ba tare da bambanci tsakanin kabilu yanki da kuma addini ba dukkanin wanda ya tauye hakkin wani sabo da bambancin jinsi, yare yanki ko addini yaci amana Kuma ya cancanci hukunci.
Sabo da haka duk wanda yayi sanadin afkar da tarzoma da tashin hankali acikin kasarmu daga shugabanni ko talakawa mace ko namiji, babba ko karami alhakin dukkanin abin da ya faru yana kansa Kuma baza mu taba yafe masa ba har abada.
Za muyi amfani da wannan dama muyi kira ga mai girma shugaban kasan nageriya da mataimakin sa kashim shetima dama su girma yan majalisar Dattijai da ta Wakilai da Ministoci da Gwamnoni da sarakuna iyaye kasa da malaman addinai da shugabbanin kungiyoyin mata da matasa akan mu zamo ma su kishin kasa da tausayin al\u2019umma da hadin kai da biyayya domin mu gudu tare mu tsira tare. Najeriya kasarmu ce wadda iyayenmu suka danka ta amana ahannun mu kada mu yi sakaci da wannan amanar ta tozarta a zamanin mu.
Dan gane da matsololin da yankin arewa yake ciki na bakin talauci da rashin aikinyi da jahilchi da yaduwar miyagun halaye a tsakanin mata da matasa da ayyukan kungiyoyin taaddanci da Suka addabi yankin mu ya zama wajibi mai girma shugaban kasa da mataimakinsa da sauran shugabannin Arewacin Najeriya da sarakuna da gwanoni da Malamai da attajirai Su hada karfi karfe wajen fitar da wannan yankin daga halin fitintinu da matsaloli da ya sami kansa shekara da shekaru saboda mahimmancinsa wajen samar da cigaban kasa baki daya.
Haka kuma muna kira ga matasan Najeriya masu albarka mu samman matasan arewacin Najeriya masu hakuri ilimi da hangen nesa masu juriya sadaukarwa da kuma jajircewa wajen abinda zai kawo cigaban kasar mu da al ummarmu ku sani kune ginshikin daukakar mu da cigaban mu kune ruhin zaman lafiyarmu da farin cikin mu kune mafi tsadar kadarorin mu kune zina rorinmu, gwalagwalen mu da azurfan mu kune abun kaunar mu kune farin cikin mu da sanyin idaniyaru kune jaruman mu gwarazon mu kuma sadaukan mu kune taurarinmu masu haskake garuruwan mu muna kaunar ku muna kishin ku muna fatan nasarar ku da cigabanku kune manyan gobe na al umman mu kune jagororinta kune shugabanninta ku kasance masu na tsuwa da fahimtar rayuwa ku zamto masu kishi masu hadin kai masu biyayya kuyi hankali da bara baragurbi masu mummunar manufa ku nisanci yan ta\u2019adda masu nufin bata kasa kuyi izina da halin da wasu kasashe suka sami kansu na fitin tinu da zubar da jini kada kuyi duk abunda ya sa bawa doka kada ku bari ma barnata su fake daku su aikata barna ku dauki matakin kare kasarku da al ummar ku tsalle daya ake fada rijiya amma ayi dubu ba\u2019a fita ba.
A karshe muna yin amfani da wannan dama wajan sanar da jamaar arewa cewa an samar da wannan cibiya mai albarka domin gudumawar ta musamman ga jama\u2019ar wannan yanki a sha\u2019anin ilimi, tattali arziki da zamantakewa, kuma muntanadin tsare tsare na musamman domin tabbatarda wannan manufofi masu albarka domin bunkasar rayuwar mata da matasa da taimakon masu rauni daga cikin alumma akan haka muna neman goyon baya jama\u2019a maza da mata,yara da manya ,shugabanni,attajirai da sauran kwararru domin samun nasarar abin da muka sa gaba.
Muna adduar Allah ya bamu zaman lafiya a kasarmu da yankin mu da garurruwanmu, Allah ya dauke mana yunwa da tsoro da kuncin rayuwa ya taimaki shugabannimmu wajen yin abin da zai tabbatar da hadin kan kasa da cigaban al\u2019ummarta, Amin summa Amin.<\/p>\n\n\n\n
Shugaban Cibiya: Almaajir Yusuf Sulaiman Sharafuddeen
Email: Yusufshareef1@gmail.com
Phone No: 08066096992, 07011536895
Date: 28\/7\/2024
inuwarjamaararewa@Gmail.com<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"
ZANGA- ZANGAR TSADAR RAYUWAZanga-zanga yancin yan kasa wanda tsarin mulki ya basu domin baiyana damuwar su ga gwamnati cikin abin da basu da wata hanyar baiyana kokensu ko kuma saboda kin karban kukansu tahanyar wakilan su.Zanga zanga nau\u2019i biyu ce zanga-zangar lumana da zanga-zanga tarzoma, kundin tsarin mulki ya amince yan kasa suyi zanga zanga […]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2303,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[61],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2377","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-feature-articles"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2377","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2377"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2377\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2378,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2377\/revisions\/2378"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2303"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2377"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2377"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2377"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}